BREAKING: ATIKU,ELRUFA'I TO TINUBU
Kalaman tsohon mataimakin shugaban Najeriyar na zuwa ne bayan Tinubu ya umarci EFCC da ta buɗe asusun ajiyar jihar Osun da ta rufe, kwana guda bayan ta ce doka ce ta ba ta hurumin rufe duk wani asusun ajiyar da ake zargi. Atiku ya ce tun da Tinubu na da hurumin bada irin wannan umarnin, to ya dace ya bada umarnin sakin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-rufa'i da ya kwashe makwanni a tsare a gidan yari kan zarge-zargen da ake yi masa.

Comments
Post a Comment